Babu Makawa APC Ce Zataci Zaben 2019 – Buhari

[ad_1]








A ranar Juma’ar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi bugun gaba tare da cika baki da cewa, jam’iyyar APC za ta yi lashe babban zabe a 2019.

Wannan bugun gaba na shugaba Buhari wani martani ne ga shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, wanda a kwana-kwanan nan ya bayyana cewa jam’iyyar adawa ta PDP ce za ta lashe zaben 2019 mai gabatowa.

Shugaba Buhari yace, ko shakka ba bu duk wadanda suka gaza wajen fahimtar hakan tare da ra’ayin rashin nasarar da jam’iyyar sa ta APC za ta yi sun hau wani doki ne na talala da babu inda zai kai su.

A ranar Larabar makon da ya gabata ne Saraki ya shaidawa mambobin jam’iyyar sa ta PDP reshen jihar Kwara cewa, nasarar zaben 2019 ta na ga jam’iyyar reshen jihar da kuma kasa baki daya.

Sai dai cikin wata sanarwa da sa hannun kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, shugaba Buhari ya bayyana cewa, nasarar da jam’iyyar APC ta yi a zabukan maye maye gurbi cikin jihohin Bauchi, Katsina da kuma Kogi shaida ce dake haskaka nasarar da jam’iyyar za ta yi a zaben 2019.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne yayin karbar bakuncin wakilan shugabannin kananan hukumomi 34 na jihar Katsina a mahaifar sa ta garin Daura.

A yayin da shugaba Buhari ke ci gaba da hutun sa na bikin babbar Sallah, yana kuma ci gaba da karbar bakuncin kungiyoyi daban-daban inda suke ziyartar sa domin taya murna ta bikin wannan lokaci.




[ad_2]

More News

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riÆ™aƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 Æ™irar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...