Babu inda zamu je daga jam’iyar PDP a cewar Saraki

Tsohon gwamnan jihar Kwara, Abubakar Bukola Saraki ya ce nan da watanni kadan za a warware rikicin da ya dabaibaye jam’iyar PDP.

Ya dage cewa kan jam’iyar a hade yake kuma har yanzu tana da karfi.

Saraki ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a wurin taron matasan jam’iyar PDP da reshen jam’iyar na jihar Kwara ya shirya a Ilorin a wani bangare na bikin cikarsa shekaru 63 da haihuwa.

Ya ce rikicin cikin gida a jam’iyar siyasa ba sabon abu bane saboda haka bai kamata a dauke shi a matsayin wani rauni ba.

” A wannan gaba ina son na fadawa mutanen mu musamman matasan jam’iyar PDP a yayin da muke kara gaba mutane da dama na cigaba da yada farfaganda cewa wace jam’iyar PDP ina kara tabbatar muku PDP tana da karfinta, cike da kuzari kuma shirye take ta bawa mara É—a kunya,” ya ce.

Tsohon shugaban majalisar dattawan ya amince cewa jam’iyyar na fuskantar kalubale amma ya bayyana kwarin gwiwa cewa nan bada jimawa ba za a warware su.

“Babu inda zamuje,kuma babu inda zaku je kuna tare da ni ina tare da ku. Duk inda zanje zamu tafi  tare PDP za ta gyara Najeriya,”ya ce.

More from this stream

Recomended