BABU AIBI DON PMB YA DAGA HANNUN GANDUJE, DAGA LAWAN M. AHMAD KARAYE

Ko kadan banga aibun buhari ba dan ya daga hannun ganduje alokacin yakin neman zabensa a jihar kano.hakan bashike nuna ina goyon bayan wannan gwamnaba.

A bangare daya al’umma nata cece-kuce bayan ziyarar yakin neman zaben da shugaban kasa muhammadu buhari yayi inda ya daga hannun Gwamnan Kano atsayin Dantakarar gwamna mai neman tazarce akano.

Alamu sun gama bayyana, wannan cece-kuce bazai taba karewa ba, duba da yadda aketa yada faya-fayai da hotunan ganduje na karbar rashawa na Dalar amurka yana zubawa a aljihu, wanda wannan abune wanda yake bako ko ince ba’a saba ji ko ganiba a tarihin siyasar nageriya.

Jama’a na tunanin Buhari bazai daga hannun Ganduje ba asakamakon furucin da yayi a kasar ingila, amma daga bisani hankalin al’umma ya sake koma kan hirarda buhari yayi awani gidan talabiji bayan bayyana shakku da tantama akan lamarin, tareda jimamin tambayarda al’ummar kano zasuyi masa akan wannan batu idan yazo yakin neman zabe.

Fakat! ya daga hannunsa, saidai aganina ba wani abu bane dukda wancan laifi da ake bincikar ganduje ko alakantasa dashi duba da yadda al’adar yakin neman zaben nageriya yake. kowanne dan takara yana daga hannun na kasa dashi idan yaje yakin neman zabe, kuma daga hannu ba shike nuna nasara ba, haka rashin dagawa ba shike nuna faduwa ba musamman idan mukayi la’akari da yanayin siyasar nigeria.

Ban sallama tunani wai cewar Ganduje zaici zabe ko akasin hakaba domin (SIYASAR KANO SAI KANO) siyasace data saba zuwa da abubuwan mamaki da al’ajabi, kuma tafi kowacce zafi da daukar hankali a afirka, shiyasa siyasar kano ta kasance (abinda ka shuka shi zaka girba) haka aketa mirgina a tarihin siyasar wannan jiha.

Lawan M. Ahmad Karaye ne ya rubuto wannan makala daga Kano.

More from this stream

Recomended