Babu ƙamshin gaskiya a batun fara dauƙar ma’aikatan Immigration

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce hukumar lura da shige da fice ta Najeriya a yanzu haka bata fara ɗaukar ma’aikata ba inda ta shawarci ƴan Najeriya da suyi watsi da duk wa ni talla da ake haɗawa a soshiyal midiya

Hukumar dake lura da ayyukan hukumomin Civil Defence, Gidajen Gyaran Hali, Hukumar Kashe Gobara da kuma Hukumar Lura Da Shige da Fice ita ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da sakataren hukumar,Jafaru Ahmed ya fitar ranar Asabar.

Sanarwar ta ce an jawo hankalin hukumar kan tallan da ake yaɗawa a kafafen sadarwar zamani ne cewa ta fara ɗaukar aikin Immigration na shekarar 2024.

Hukumar ta ce wannan aikin wasu ɓata gari ne dake neman zambatar yan Najeriya.

“Sanarwar ɗaukar aikin jabu ce kuma bata fito daga hukumar ba,” a cewar sanarwar.

More News

Mutane 11 Sun Mutu A Wani Hatsarin Mota A Kano

Mutanen da basu gaza 11 ne ba aka tabbatar da sun mutu a yayin da wasu 16 suka jikkata mutum ɗaya kuma ya tsira...

Ƙasar Amurika ta fara shirin kwashe sojojinta daga Nijar

Gwamnatin kasar Amurka ta fara shirin janye dakarunta daga jamhuriyar Nijar kamar yadda kafar yaɗa labarai ta CBS ta bada rahoto. Wani jami'in ma'aikatar wajen...

Sojoji sun kashe ƴan ta’adda biyu tare da gano makamai a jihar Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya sun kashe wasu ƴan ta'adda biyu a ƙauyen Kana dake ƙaramar hukumar Biu ta jihar Borno. A wata sanarwa ranar Asabar...

An halaka mutane 6 a wani faɗa tsakanin ƴanbindiga da ƴanbanga

Mutane 6 ne suka rasa rayukansu a wata arangama da aka yi tsakanin ‘yan bindiga da ’yan banga da aka fi sani da ‘Yan...