
Babban sifetan yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya gana da tsofaffin jami’an yan sandan da suka yi ritaya.
Ganawar ta gudana ne a hedkwatar rundunar dake Abuja kuma an yi ta ne dai-dai lokacin da tsofaffin jami’an suka gudanar da zanga-zanga kan yadda ake biyansu hakkokinsu na fansho.
Jami’an sun koka kan yadda ake biyansu abun da bai taka kara ya karya ba a matsayin fansho a matsayin fansho da garatuti.
Kawo yanzu dai babu wata sanarwa da rundunar ta fitar kan abun da aka cimma a yayin ganawar.