Mai rikon mukamin Babban sifetan ƴansandan Najeriya, Muhammad Adamu ya bayar da umarnin dakatar da zirga-zirgar ababen hawa daga karfe 6:00 na safiyar ranar Asabar ya zuwa karfe 06 na yammacin ranar.
Mai magana da yawun rundunar, DCP Frank Mba shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
Mba ya bayyana cewa an dauki wannan mataki ne domin kare lafiyar mutane da dukiyoyinsu da kuma inganta tsaro a kasa ya yin zaben shugaban kasa da za a gudanar ranar Asabar.
Ya kara da cewa hakan zai taimakawa jami’an tsaro wajen saka ido akan zaɓen wajen hana bata gari kawo tasgaro a zaɓen.