Babban Hafsan Tsaro na ƙasar, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa ya kamata ‘yan Najeriya su nuna godiya bisa irin ci gaban da ake samu wajen yaƙi da matsalar tsaro a ƙasar.
Janar Musa ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da yake amsa tambayoyi a cikin shirin Politics Today na tashar Channels Television.
Ya ce rundunar sojojin Najeriya ta samu gagarumin nasara a baya-bayan nan, ciki har da cafke ɗan marigayi wanda ya kafa ƙungiyar Boko Haram da kuma wasu manyan kwamandojin ƙungiyar Ansaru.
A cewarsa, ba za a iya kawar da matsalar tsaro gaba ɗaya cikin ɗan gajeren lokaci ba, domin babu wata ƙasa a duniya da ke da cikakkiyar zaman lafiya.
Ya ce: “Ina ganin ya kamata mu yi godiya sosai saboda abubuwa suna ƙara tafiya daidai. Ban yi imani akwai wata ƙasa da take da zaman lafiya kashi 100 cikin ɗari ba. Shekaru 16 kenan muna fama da wannan matsala; ba abu ba ne da za a kawo ƙarshensa cikin shekaru biyu kawai. Amma zan iya faɗa muku cewa mun samu gagarumin ci gaba. Mun ambaci kwamandojin Ansaru da aka kama, wannan na daga cikin manyan nasarorin da aka samu. Samun waɗannan mutane biyu ya nuna tsantsar shirin da aka yi,” in ji shi.
Babban Hafsan Tsaron Najeriya: ‘Ya Kamata ‘Yan Najeriya Su Nuna Godiya Saboda Ci Gaban Tsaro’
