Babban Alƙalin Jihar Katsina, Mai Shari’a Musa Danladi, ya bayar da beli ga fursunoni 91 tare da sallamar wasu hudu gaba ɗaya, yayin wani shirin rage cunkoson gidajen gyaran hali da aka gudanar a farkon kwata na shekarar 2025.
Yayin taron da aka gudanar a Medium Security Custodial Centre da ke Katsina a ranar 20 ga Maris, 2025, Mai Shari’a Danladi ya bayyana cewa Kwamitin Rage Cunkoson Gidajen Gyaran Hali ya yi nazari sosai kan shari’o’in da suka dace da sakin fursunonin.
Ya ce tsawon lokacin da suka shafe a tsare, matsalolin lafiya na daga cikin abubuwan da aka yi la’akari da su wajen bayar da belin da kuma sallamar wasu gaba ɗaya.
Mai Shari’a Danladi ya kuma sanar da cewa daga yanzu, za a rika rubuta sunaye da ɗaukar hotunan mutanen da aka saki domin tabbatar da ingantaccen tsarin rajista da bin diddigi.
Yayin da yake yi wa fursunonin da aka saki nasiha, ya ja hankalinsu da su guji komawa aikata laifuka, yana mai cewa idan suka sake yin kuskure, watakila ba za su samu irin wannan dama ba a nan gaba.
A nasa bangaren, Kwamandan Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Katsina, CC Umar Baba, ya yabawa wannan shiri, yana mai cewa yana rage cunkoso, inganta yanayin gidajen gyaran hali, da kuma bai wa fursunoni damar samun tarbiyya mai kyau.
Ya kuma bukaci alƙalai da magistratai da su rika daukar hanyoyin hukunta mutane ba tare da an tsare su ba, domin hana cunkoso a gidajen gyaran hali da kuma bai wa waɗanda suka yi kuskure damar samun gyara da komawa cikin al’umma.
Babban Alƙalin Jihar Katsina Ya Saki Fursunoni 95
