Sabon ƙaramin ministan ma’aikatar gidaje da bunƙasa birane, Yusuf Abdullahi Ata ya ce babban kudirinsa shi ne yasa jam’iyar APC ta lashe zaɓe a jihar Kano a shekarar 2027.
Ata ya bayyana haka ne a ƙarshen mako lokacin da yake zantawa da ƴan jaridu a Kano bayan da aka rantsar da shi a matsayin minista.
Ministan gidajen ya ce dalilin siyasa ne ya sa aka naɗa shi minista.
“APC ta rasa Kano yanzu kuma za ta ƙwace Kano.Babbar matsalar dama ita ce Kano ta tsakiya kuma daga nan na fito,” ya ce .
“Duk da ina minista zan cigaba da zama a wannan mazaɓar. Zamu yi aiki tuƙuru domin ganin APC ta lashe zaɓen Kano a shekarar 2027,” ya ce.
“An tura ni ma’aikatar gidaje da bunƙasa birane. Zan yi aikina amma zan riƙa zuwa Kano duk mako domin yin aikin ƙwace iko da jihar a shekarar 2027.”