Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na kawo ƙarshen ta’addanci da ayyukan ‘yan fashi a Arewacin Najeriya.
Ya ce ba zai yarda wani ɓangare na ƙasar ya ci gaba da fuskantar zubar da jini ba yayin da gwamnatin tarayya ke kallo. Tinubu ya faɗi hakan ne a ranar Asabar a lokacin bikin cika shekaru 25 na ƙungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) da aka gudanar a Kaduna.
Shugaban ya samu wakilci daga Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas.
Tinubu ya ce ya gaji wani mawuyacin halin tsaro, amma ya kuduri aniyar dawo da zaman lafiya. Ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta dakatar da durƙushewar tattalin arzikin yankin Arewa da aka dade ana fama da shi.
Ya ambaci fara hako mai daga filayen Kolmani da sauran damammaki a matsayin hanyoyin farfaɗo da tattalin arzikin yankin.
Ba Zan Bari A Ci Gaba Da Zubar Da Jini A Arewa Ba, Inji Tinubu

