Ba zai yiyu a kirkiri sababbin jihohi ba yanzu, cewar mai magana da yawun majalisar dattawa

Yemi Adaramodu mai magana da yawun majalisar dattawa ya ca majalisar dattawan baza ta bada shawarar ƙirƙirar sabbin jihohi ba a yanzu.

Adaramodu ya fadi haka ne lokacin da ya ke magana da yan jaridu a garin Ilawe mahaifarsa dake jihar Ekiti.

Ya ce kawo yanzu majalisar dattawan ta karbi bukatar ƙirƙirar sababbin jihohi 61 daga shiyoyi 6 dake ƙasarnan.

Dan majalisar dattawan ya ce majalisar ita kadai bata da ikon ƙirƙirar sabuwar jiha inda ya bayyana matakan da ake bukatar abi  sun hada da da sake tantance “alkaluman bayanan yawan jama’a, taswira da kuma na tarihi,”

” Na farko dai majalisar dattawa ita kadai baza ta iya kirkirar jiha ba bukata irin haka dole ne a duba ta a lokacin gyaran kundin tsarin mulki,” ya ce.

Adaramodu ya ce bukatar ƙirƙirar sababbin jihohi an mika su a hukumance a yayin taron ganawa da jama’a kan gyaran tsarin mulki da ya gudana a fadin ƙasarnan.

Ya kara da cewa dukkanin buƙatar da aka gabatar za a karba a kuma sake dubata a kwamitin gyaran kundin tsarin mulkin da shugaban majalisar dattawa, Barau jibrin yake jagoranta.

More from this stream

Recomended