Ba za mu iya biyan naira 60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba

Gwamnonin jihohin Najeriya 36 sun ce kudirin biyan mafi karancin albashi na Naira 60,000 da gwamnatin tarayya ta yi ba zai dore ba kuma ba za su iya aiwatarwa ba.

Wata sanarwa da mukaddashin daraktan yada labarai da hulda da jama’a na kungiyar Mrs.  Halima Ahmed, ta bayyana cewa idan aka ba su izinin tashi sama, jihohi da dama za su yi amfani da duk wani kason da suke samu daga asusun tarayya wajen biyan albashin ma’aikata ne.

Gwamnonin sun yi kira ga mambobin kwamitin uku da su amince da mafi karancin albashin da zai yi daidai kuma ya dore.”

Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta amince cewa za a kara sabon mafi karancin albashi. 

Kuma Kungiyar ta jajantawa kungiyoyin kwadago a kokarinsu na neman karin albashi.

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya ƙirƙiri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a ƙara wa ƴan bautar ƙasa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...