
Asalin hoton, BuhariSalau
Gwamnatin Najeriya ta ce sai nan da shekarar 2025 za a kammala aikin hanyar Abuja zuwa Kano da aka fara a 2018.
Ministan ayyuka da gidaje Babatunde Fashola ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki a Kaduna, na wani babban ayari na gwamnatin tarayya.
“Nan da shekarar 2022 ne za a kammala hanyar da ke tsakanin Kaduna da Zaria, wanda wannan babban ci gaba ne.
“A 2023 za a kammala hanayar da ta tashi daga Kaduna ta dangane ga Kano, sai kuma a 2025 za a kammala hanyar Abuja zuwa Kano baki É—ayanta,” in ji Fashola.
Tawagar gwamnatin tarayyar ta ziyarci aikin da ake yi tsakanin Kaduna zuwa Kano inda ta ce ta gamsu da yadda ake gudanar da aikin, duk kuwa da cewa wasu al’ummar Æ™asar na Æ™orafi kan yadda wannan aiki ke tafiyar hawainiya.
Cikin tawagar har da shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya Ibrahim Gambari, wanda ya wakilci Shugaba Muhammadu Buhari, ya ce ” mun gamsu da ingancin aikin a wuraren da aka kammala, duk da cewa akwai ‘yan matsaloli.”
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, na cikin tawagar sai dai ra’ayinsa ya sha bamban da na ministan ayyukan, in da ya ce ” za’a kammala aikin cikin wannan lokaci da shugaba Buhari ke jagorantar Najeriya.”
Matsalolin kan hanyar
Wani Abu da masu bin hanyar ke ƙorafi a kai shi ne rashin tabbas da duk wani mai bin hanyar ke fuskanta har sai ya ga ya isa inda ya nufa.
Sakataren ƙungiyar direbobin sufuri ta NURTW na jihar Kaduna Alhaji Bature Yusuf Sulaiman, ya ce abin takaici ne yadda ake jan ƙafa a wannan aiki.
“Duka direbobinmu na cikin matsala sakamakon É—aukar lokaci da wannan hanya ta yi, a wasu lokutan sai dai direba ya yi hakuri ya zaÉ“i rami mai gwara-gwara ya faÉ—a amma akwai inda ba ka isa ka wuce ba sai ka shiga rami.
“Matsala ta biyu ita ce É“arayi na amfani da damar nan suna kama mutane su yi garkuwa da su abu ne da ke faruwa kusan ko wacce rana, wannan ya sanya mutane cikin wata damuwar ta daban,” in ji Alhaji Bature.
Ko a ƙarshen makon da ya gabata sai da masu garkuwa da mutane suka tare hanyar tare da kama mutane da dama, baya ga harbin motar mutane da suke yi idan suka ƙi tsaywa.
Waiwaye
Asalin hoton, NIGERIA GOVT
Hanya ce mai nisan kilomita fiye da 400 da Ministan makamashi da ayyuka da kuma gidaje ya kaddamar
Gwamnatin Najeriya ta ware kuÉ—i fiye da naira biliyan 155 domin aiwatar da aikin gyaran hanyar mai nisan kilomita fiye da 400.
A 2017 ne gwamnatin kasar ta amince da aikin bayan wani taron majalisar ministocin kasar da aka yi karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari.
Hanyar dai ta dade da lalacewa, al’amarin da kan janyo haÉ—uran motoci a waÉ—ansu lokuta tare da asarar rayuka.
A shekarar 2017 ne gwamnatin kasar ta gyara wani bangare na hanyar wato tsakanin Abuja zuwa Kaduna lokacin da aka rufe filin jirgin saman Abuja domin hanyar jirgi da za a gyara.
Sai dai daga bisani hanyar ta kara koma gidan jiya.
Kalamai masu karo da juna
A lokacin da aka ƙaddamar da wannan aiki, Ministan lantarki da ayyuka da kuma gidaje na Najeriya Babatunde Fashola ya ce an ware kuɗaɗe da suka kai naira biliyan 155 domin aiwatar da aikin.
Malami ya ce za a yi amfani da kuÉ—aÉ—en wajen kammala ayyuka a sassan Najeriya da suka haÉ—a da hanyar Legas zuwa Ibadan da hanyar Abuja zuwa Kano da kuma gadar Neja.
A gefe ɗaya kuma wasu kafafen yaɗa labaran ƙasar na cewa, ba a bai wa kamfanin da yake aikin kuɗinsa ba ne baki ɗaya, kamar yadda aka saba yi a yarjejeniyar kwangila.
Wannan dalilin ya sanya ita ma gwamnatin tarayya ba ta matsawa kamfanin kan sai ya kammala aikin ba.
Ina naira miliyan 155 da aka ware a 2018, ina kuma kuÉ—aÉ—en da aka karÉ“o daga Amurka da ake zargin Abacha a wawure? wannnan ce tambayar da mafi yawan ‘yan Æ™asar ke yi.