Jagoran jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa ba za a iya saya ko rinjayar sa da kuɗi a harkar siyasa ba, yana mai jaddada cewa shi “ba shi da farashi”.
Kwankwaso ya yi wannan furuci ne yayin da yake tsokaci kan wasu abubuwan da ke faruwa a siyasar Jihar Kano, inda ya taɓo batutuwan biyayya, cin amana da kuma yanayin siyasa gaba ɗaya a jihar.
Tsohon gwamnan ya ce siyasa na zuwa da riba da asara, amma cin amana na haddasa fushin jama’a, musamman a wannan lokaci da ’yan Najeriya da dama ke fama da matsalar tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziki.
A cewarsa, masu watsi da ƙa’idoji saboda ribar kai suna kan jefa kansu cikin tsari na siyasa da ba su da mafita mai kyau.
Kwankwaso ya bayyana cewa cin amana na ci gaba da lalata amincewar jama’a ga wasu tsare-tsaren siyasa, yana mai cewa hakan na daga cikin dalilan da ke haifar da raguwar goyon bayan jama’a, musamman sakamakon gazawar shawo kan matsalolin tsaro da tattalin arziki.
Ya ƙaryata ra’ayin da ke cewa duk ɗan siyasa ana iya sayen sa, yana mai jaddada cewa mutuncinsa ba na sayarwa ba ne.
Jagoran NNPP ya kuma bayyana siyasar Kano a matsayin ta musamman, yana mai cewa masu zaɓe a jihar suna da ilimin siyasa kuma ba su da sauƙin rinjaya da kuɗi ko kyaututtuka.
Ba Wanda Zai Iya Sayata A Siyasa – Kwankwaso

