Ba ni da burin a raba masarautar Kano – Sarkin Bichi

BBC

Sabon sarkin Bichi Mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce ya kwan da sanin cewa masarautar Kano na taimakawa wajen hada kan al’umma, don haka ba shi da wani buri na ganin an rarraba masarautar mai tsohon tarihi.

“A rayuwata, ba ni da wani buri na ga an rarraba masarautar Kano, domin mun san tana kawo hadin kai na al’umma baki daya,” sarkin ya shaida wa BBC jim kadan bayan kammala ‘taron godiya’ da gwamnatin jihar ta shirya ranar Asabar

Sarki Aminu Ado na daya daga cikin sabbin sarakuna guda hudu da gwamnatin ta nada bayan ta kirkiri karin masarautu “don rage matsalolin ci gaba da da suka yi nauyi kwarai da gaske a halin yanzu ta yadda ba za mu iya barin wadannan al’amura na ci gaba a hannun masarauta mai dunkule daya ba,” a cewar Gwamna Ganduje.

Sarkin Bichi ya ce duk da ba shi da burin raba masarautar, amma wasu dalilai da gwamnati ta hanga har kuma a kawo wannan sauyi, “to babu wani abu da al’umma za su yi, sai dai su karbi wannan yanayi da Allah ya kawo”.

Kafin nadinsa a matsayin sabon sarki, Aminu Ado Bayero na rike da sarautar Wamban Kano ne a masarautar Sarki Sanusi na II.

Baya ga Sarki Aminu na Bichi, Gwamna Ganduje ya kuma tabbatar da nadin Sarkin Karaye, Dr Ibrahim Abubakar da Sarkin Rano, Alhaji Tafida Abubakar Ila da kuma Sarkin Gaya Alhaji Ibrahim Abdulkadir.

Wasu dai na cewa gwamnatin Kano ta rarraba masarautar Kano ce don karya karfin Sarki Muhammadu Sanusi na II, wanda aka yi imani suna takun-saka da gwamnatin jihar, ko da yake, ta fito ta musanta haka.

Wata babbar kotu dai ta ba da umarni a dakatar da duk wani mataki na tabbatar da sarakuna har sai a saurari waa kara tare da yin hukunci kan wata bukata da aka shigar gabanta dangane da kirkirar sabbin masarautun.

Sai dai Gwamnan Kano ya ce zuwa lokacin da suka yi taron, gwamnatinsa ba ta samu wani umarni daga kotu ba, kuma da ma tun da maryacen Juma’a suka bai wa sabbin sarakunan takardun kama aiki.

Shi dai Sarki Aminu na Bichi yana fatan al’umma za su karbi wannan al’amari da ya ce: “Allah ne ya kawo, kuma a yi addu’ar Allah sa haka ne ya fi alheri”.

Ya ce babu wani dalili da zai sa a samu baraka tsakaninsa da Sarkin Kano, don kuwa sun ba shi duk irin gudunmawar da ta kamata, lokacin da Allah ya ba shi sarauta bayan rasuwar mahaifinsa, Sarki Ado Bayero.

“Saboda haka ni na yarda da Ubangiji ne yake shirya wadannan abubuwa. Kuma shi ya shirya ya ba wa mai martaba sarautar gidanmu, kuma muka goya masa baya, mukai masa addu’a, muka ba shi dukkan shawarwari, a cewar sabon sarki.

More News

EFCC na neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (Economic and Financial Crimes Commission) ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin...

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Sojoji Sun Ceto Lydia Simon ĆŠaya Daga Cikin Ćłan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon É—aya daga cikin...

Gwamna da ƴansanda sun daƙile yunkurin EFCC na kama Yahaya Bello

A ranar Laraba ne Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, ya dakile wani yunkurin da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta...