Ba a biya kudi ba kafin sako ‘yan matan Dapchi – Gwamnatin Najeriya

[ad_1]

A watan Fabrairu aka sace daliban daga makarantarsu da ke Dapchi, a jihar Yobe

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

A watan Fabrairu aka sace daliban daga makarantarsu da ke Dapchi, a jihar Yobe

Gwamnatin Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa ta biya mayakan Boko Haram ‘makudan kudin fansa’ kafin su sako ‘yan matan Dapchi.

Wani rahoto ne da aka gabatar a gaban kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa sai da gwamnatin kasar ta biya “makudan kudi” don kubutar da ‘yan matan makarantar sakandaren garin Dapchi.

Har ila yau rahoton ya ce irin wadannnan kudaden da ake biya suna kara taimakawa wajen wanzuwar ayyukan ta’addanci a yankin Tafkin Chadi.

Fiye da ‘yan mata 100 ne wani bangare na kungiyar Boko Haram ya sace a wata makarantar sakandaren garin Dapchi a jihar Yobe a watan Fabrairun da ya gabata.

Sai dai kimanin ‘yan mata 105 kungiyar ta saki daga bisani, amma kawo yanzu akwai guda da ta rage a hannun mayakan kungiyar wato Leah Sharibu.

Bayan soko ‘yan matan dai Ministan Yada Labaran kasar Lai Mohammed ya shaida wa manema labarai cewa, ba a biya ko da sisin kwabo ba, gabanin sako ‘yan matan a watan Maris din da ya gabata.

Hakazalika bayan fitar rahotan Majalisar Dinkin Duniyar, a ranar Alhamis ministan ya kara jaddada matsayinsa na farko.

“Bai kamata wani ya ce Najeriya ta biya kudi kafin ceto ‘yan matan Dapchi, ba tare da nuna kwararan hujjoji da za su tabbatar da hakan ba,” kamar yadda wata sanarwa da mai taimaka masa Segun Adeyemi ya fitar ta ce.

Lai ya kalubanci duk wani da ke hujjoji da ke nuna cewa an biya kudin da ya bayyana wa duniya hakan.

Har ila yau ya ce “to idan kuma babu hujjojin da za su gasgata hakan to abin ya zama shashi-fadi ke nan.”

Hakkin mallakar hoto
Amsami Ali

Image caption

An kai matan Abuja a cikin motoci

  • A ranar 19 ga Fabrairu aka sace ‘yan matan
  • Dalibai 110 aka sace a makarantar Dapchi
  • An sace su kwana daya bayan sojoji sun fice
  • An shiga rudani kan sace ‘yan matan
  • Da farko an ce ‘yan matan sun shiga daji ne domin buya
  • Sai da aka dauki tsawon mako daya kafin gwamnati ta amince an sace su
  • Gwamnatin Yobe ta yi ikirarin ceto ‘yan matan, kafin daga baya ta nemi afuwa
  • Bangaren Abu Musab al-Barnawi ne ake tunanin sun sace ‘yan matan
  • Boko Haram ba ta fito ta yi ikirarin sace ‘yan matan ba
  • Sace ‘yan Matan Dapchi ya tuna wa duniya da ‘yan matan Chibok
  • Wannan ya nuna har yanzu Boko Haram barazana ce
  • Sun gana da Shugaba Buhari

Jam’iyyar PDP mai hamayya a kasar ta yi zargin cewa jam’iyyar APC da fadar shugaban kasa ne suka kitsa sace matan domin cimma burin siyasa.

Sai dai APC ta musanta zargin, tana mai cewa idanun PDP sun rufe ta kasa fahimtar irin nasarar da take samu a yaki da Boko Haram.

Hakkin mallakar hoto
Amsami Ali

Image caption

Sun kwashe sama da wata daya a hannun mayakan Boko Haram

[ad_2]

More News

Zanga-zanga: An jibge ƴan sanda 4200 a Abuja

Rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja ta tura ƴan sanda 4200 gabanin zanga-zangar da za a gudanar a cikin watan Agusta. Kamar yadda masu shirya...

Kamfanin NNPC ya shirya daukar karin ma’aikata

Kamfanin mai na Nigerian National Petroleum Company Limited ya shirya daukar karin ma’aikata.Kakakin kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya tabbatar da hakan a wata...

Ya kamata matasa su yi haƙuri zanga-zanga ba ita ce mafita ba – Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli ya ce matasa su ƙara haƙuri da gwamnatin tarayya su janye zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a...

Zanga-zanga: Tinubu ya gana da gwamnonin APC

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyar APC. Taron ganawar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa ta...