
Asalin hoton, Reuters
Yanzu haka yan sanda sun killace sha tale-talen Schwedenplatz
Mahara dauke da bindigogi sun buda wuta a sassa shida na garin Vienna, inda su ka kashe mutun daya tare da jikkata wasu da dama kamar yadda yan sanda su ka sanar.
An fara kaddamar da harin ne da misalin karfe 8;00 na yammacin Litinin.
Shugaban gwamnatin Austria Sebastian Kurz ya yi Allah-wadai da harin.
Mr Kurz ya ce an samu nasarar kashe daya daga cikin maharan.
Yanzu haka yan sanda na kan neman akalla mahari daya ruwa a jallo kamar yadda ministan harkokin cikin gida ya sanar.
Harbe harben sun faru ne a tsakiyar Vienna kusa da wani coci, to amma babu tabbas ko ita ce a ka hara.
An kashe mutun daya nana take, yayin da wata mata ta cika a asibiti bayan da ta samu raunuka kamar yadda mai garin Vienna Michael Ludwig ya ce.
Asalin hoton, Reuters
An fara kaddamar da harin ne da misalin karfe 8;00 na yammacin Litinin.
Yanzu haka mutun 14 na jinya a asibiti kuma shida daga ciki sun samu munanan raunuka.
Harin ya zo a na dab da shiga kullen Korona, a dai dai lokacin da yan kasar su ka hadu a gidajen abinci da mashaya kafin su shiga kullen da za shafe watan Nuwamba a na yi.
Shugabannin kasashen Turai sun yi Allah-wadai da harin Vienna, cikinsu har da Firanministan Burtaniya Boris Johnson.
(BBC Hausa)