Atiku ya ziyarci Obasanjo

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo a gidansa dake Abeokuta.

Atiku ya kasance mataimakin Obasanjo daga shekarar 1999-2007.

Paul Ibe mai taimakawa Atiku kan watsa labarai ya ce mutanen biyu sun gana ne ranar Litinin da rana.

Atiku ya samu rakiyar tsohon gwamnan jihar Cross River, Liyel Imoke, Aminu Tambuwal tsohon gwamnan Sokoto da kuma Sanata Abdul Ningi.

Wata majiya dake da alaƙa da taron ta ce ganawar na da alaƙa da batun dunƙulewar ƴan adawa guri guda gabanin zaɓen shekarar 2023.

Acikin watan Nuwamba ne Atiku ya shawarci ƴan adawa da su kasance ƙarƙashin inuwa guda inda ya ce Najeriya na buƙatar jam’iyar adawa mai ƙarfi.

More from this stream

Recomended