
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ziyarci Rauf Aregbesola tsohon gwamnan jihar Osun a gidansa dake jihar.
A wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter a baya an nuna Atiku yana fitowa daga mota a harabar gidan inda tsohon gwamnan ya fito ya tarbe shi.
Mutanen biyu sun shiga cikin tare da wadanda suke musu rakiya.
“Lokacin karin kumallo a gidan gidan tsohon gwamnan jihar Osun, Engr Rauf Aregbesola,” Atiku ya rubuta a kasa bidiyon da ya wallafa.
An kori Aregbesola daga jam’iyar APC a jihar Osun cikin watan Janairu bayan da aka zarge shi da yiwa jam’iyar zagon kasa.
Atiku ya kuma ziyarci birnin Akure a jihar Ondo inda ya halarci bikin nadin, Clement Adesuyi a matsayin basaraken gargajiya na Ijesaland.