Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya sake sukar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya bayyana ta a matsayin barazana mafi girma ga dimokuradiyyar Najeriya tun bayan dawowar mulkin farar hula.
Atiku ya yi wannan furuci ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, tare da yin ziyarar jaje ga tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir el-Rufai, wanda aka kai masa hari lokacin kaddamar da jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Kaduna.
A cewar dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023:
“Yau da yamma na kai ziyarar jaje ga tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir el-Rufai, bisa harin da wasu da APC ta dauko suka kai masa a yayin kaddamar da jam’iyyar ADC a Kaduna.
“Na jaddada cewa ayyukan gwamnatin APC da Tinubu ke jagoranta suna haifar da babbar barazana ga dimokuradiyyar mu tun bayan dawowar mulkin farar hula.
“Abin damuwa shi ne yadda wannan gwamnati ta koma yin kama-karya sosai,” in ji shi.
Atiku ya kara da cewa irin wannan yanayi na nuna karfi da zalunci ba zai amfani kasar ba, illa dai kara raunana tsarin dimokuradiyya da ‘yancin ‘yan kasa.
Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tinubu Da Yin Kama-Karya
