Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu bisa gazawarta wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya, musamman a Arewa.
Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa wajen watsa labarai, Paul Ibe, ya fitar, inda ya nuna damuwarsa kan yawaitar hare-haren ta’addanci a jihohin Plateau da Borno.
A ranar Lahadi, kimanin mutum 47 ne suka rasa rayukansu a harin da aka kai garin Zike da ke yankin Kimakpa na ƙaramar hukumar Bassa a jihar Filato. Wannan harin ya zo ne kasa da mako guda bayan makamancinsa a ƙaramar hukumar Bokkos, inda mutane da dama suka mutu tare da lalata dukiyoyi.
Atiku ya ce hare-haren da ke gudana a jihar Borno da kewaye, musamman yadda Boko Haram ke kwace ƙananan yankuna, abin takaici ne da ke nuna gazawar tsarin tsaro da kuma kayan aikin da gwamnatin Tinubu ke amfani da su.
Ya ce: “Wannan yawaitar hare-haren da kuma yadda masu tada ƙayar baya ke aikata ta’asa ba tare da hukunta su ba, alama ce ta gazawar manufofin tsaro na wannan gwamnati.”
Ya kuma bayyana cewa, rashin gurfanar da ‘yan ta’adda da ke tsare tun shekarar 2016 yana kara wa masu aikata kisan kiyashi kwarin guiwar cigaba da aika-aikansu.
Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da gazawa a harkar tsaro sakamakon harin Borno da Plateau
