Atiku ya yi rijista da jam’iyar ADC

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi rijista da jam’iyar ADC a hukumance.

Atiku ya yi rijista da jam’iyar ta ADC tare da karɓar katin jam’iyar a mazabar Jada 1 dake karamar hukumar Jada ta jihar Adamawa a ranar Litinin.

A cikin watan Yuli ne Atiku ya sanar da ficewarsa daga jam’iyar PDP inda ya yi zargin cewa jam’iyar ta kauce daga kan akidun da aka kafa ta akai.

Atiku dake da shekaru 78 shi ne wanda ya yiwa jam’iyar PDP takara a zaɓen shekarar 2023.

A cikin watan Mayu wasu jiga-jigan yan adawa suka amince su shiga jam’iyar ADC inda za suyi amfani da gwadaben jam’iyar wajen kalubalantar jam’iyar APC a zaɓen shekarar 2027.

More from this stream

Recomended