Atiku ya hadu da wasu jiga-jigan jam’iyar APC

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya hadu da wasu jiga-jigan jam’iyar APC.

Haduwar ta su ta faru ne a lokacin da tsohon mataimakin shugaban kasar ya kai wa, Alhaji Dahiru Mangal ziyarar ta’aziyar rasuwar mahaifiyarsa.

Cikin wadanda suka samu gaisawa da tsohon mataimakin shugaban kasar akwai, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, shugaban rikon jamiyar APC, Mai Mala Buni da kuma gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari.

Atiku yayi adduar Allah ya jikan marigayiyar ya kuma bawa iyalanta hakurin jure wannan babban rashi.

More from this stream

Recomended