Atiku ya bayar da tallafin miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya bayar da gudunmawar naira miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

A ranar Talata ne ambaliyar ruwa ta raba miliyoyin mutane da gidajensu a unguwannin   Fori, Galtimari, Gwange, da kuma  Bulabulin dake Maiduguri.

Hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasa, NEMA ta ce mutane 30 aka tabbatar sun mutu yayin da sama da mutane 400,000 suka rasa gidajensu sanadiyyar ambaliyar ruwan a birnin na Maiduguri.

Tuni gwamnatin jihar Borno ta buɗe sansanonin ƴan gudun hijira domin tsugunar da mutanen da abun ya shafa.

Da yake magana a lokacin ziyarar a ranar Lahadi a Maiduguri tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana ambaliyar a matsayin wata babbar masifa.

” Duk da cewa mai gabatar da taro ya faɗi dalilin zuwan mu. Ina so ku sani cewa duk abun da ya shafi Borno to ya shafe ni,” a cewar Atiku.

Ya ce sun je garin ne shi da tawagarsa domin jajantawa Shehun Borno, gwamnatin jihar dama al’umma baki ɗaya kan iftila’in da ya faru.

More from this stream

Recomended