Atiku Da Kashim Shettima Sun Haɗu A Wurin Ɗaurin Aure

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar sun haɗu a wurin ɗaurin aure a Abuja ranar Asabar.

Irin wannan haɗuwa da ba kasafai ba ita ce irinta ta farko tun bayan da aka fara sauraron karar zaben 2023.

Atiku wanda ya yi takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyar PDP a yanzu haka na kalubalantar nasarar da jam’iyar APC mai mulki ta samu wanda a karkashinta Tinubu da Shettima suka yi takara.

Amma a wurin ɗaurin auren Mohammed (Ameer) Bunu da Ikramullah Jamal Arabi dukkanin mutanen biyu sun jingine banbancin siyasar dake tsakanin su inda suka yi musabaha.

More from this stream

Recomended