Atiku Abubakar Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP).

A cikin wata sanarwa da ya fitar mai dauke da kwanan watan 14 ga Yuli, 2025, Atiku ya ce: “Ina sanar da jama’a ficewata daga jam’iyyar PDP ba tare da ɓata lokaci ba.”

Atiku ya bayyana godiyarsa ga jam’iyyar bisa damar da ta ba shi a baya. A cewarsa: “Ina son yin amfani da wannan damar na bayyana godiyata ga jam’iyyar ta PDP bisa irin damarmakin da ta ba ni: Na yi mataimakin shugaban ƙasa karo biyu a jam’iyyar sannan na yi takarar shugaban ƙasa karo biyu a PDP. A matsayina na ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar ta PDP, saboda haka akwai sosa rai ƙwarai dangane da ɗaukar wannan hukunci.”

Dangane da abin da ya sa ya yanke shawarar barin jam’iyyar a wannan lokaci, Atiku ya ce: “Dole ne na raba gari da jam’iyyar a yanzu bisa la’akari da yadda PDP ta sauka daga harsashinta na asali da muka fata domin shi. Lallai abin da sosa rai ficewa daga cikinta bisa dogaro da yadda ba za mu daidaita ba da jam’iyyar.”

Ficewar Atiku daga PDP na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da hasashen sauyin salon siyasa a jam’iyyun Najeriya, musamman yayin da shirye-shiryen babban zaben 2027 ke karatowa.

More from this stream

Recomended