ASUU Ta Ki Amincewa Da Tayin Gwamnati

Kungiyar malaman jami’a ta Najeriya, ASUU, ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da yajin aikin sai baba-ta-gani bayan ta kasa samun matsaya da gwamnati kan bukatun kungiyar.

ASUU da ta shafe fiye da wata daya tana yajin aiki ta yi watsi da tayin gwamnatin tarayya na biyan wasu daga cikin bukatun kungiyar.

Rahotanni sun ce gwamnatin tarayya ta saki kudi kusan naira biliyan 15.4 domin biyan jami’o’in na gwamnati. Kuma Shugaba Buhari ya amince a biya malaman jami’oin kudadensu na ariyas naira biliyan 20 da suke bi daga 2009 zuwa 2002.

Sai dai kuma shugaban kungiyar malaman jami’o’in Biodun Ogunyemi ya yi watsi da kudirin na gwamnati, kamar yadda jaridar PremiumTimes ta ruwaito.

Mista Ogunyemi ya nuna cewa kudaden sun yikadan daga cikin kudaden alawus da mambobinkudingyar suke neman gwamnati ta biya su.

Ya ce ya kamata gwamnati ta fayyace adadin kudaden da take nufi na malaman jami’oin da kuma hakkin na wadanda ba malamai ba donkaucewa rikicin da ya biyo baya a 2017 lokacin da gwamnatin da saki biliyan N22.9.

Shugaban malaman jami’o’in ya jaddada cewa biliyan N220 suke bukata daga gwamnati daga tiliyan 1.1 da suke bi.

A ranar 4 ga watan Nuwamba ne kungiyar ASUU ta shiga yajin aiki bayan kasa fahimtar juna tsakaninta da ministan ilimi Adamu Adamu kan bukatunta.

Kungiyar ta zargi gwamnatin Najeriya da gaza aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta yanayin aiki a jami’o’in, da kuma rashin biyan mambobinta kudaden alawus da wasu sauran bukatunta.

More from this stream

Recomended