ASUU ta dakatar da yajin aiki a Jami’ar Kaduna

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) reshen Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) ta dakatar da yajin aikin da ta fara a ranar 18 ga Fabrairu.

Shugaban ASUU na KASU, Dr. Peter Adamu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya tabbatar da cewa an yanke shawarar janye yajin aikin ne a ranar Asabar.

Adamu ya bayyana cewa dakatar da yajin aikin ya biyo bayan kokarin da gwamnatin Jihar Kaduna ta yi na warware matsalolin kudi da kungiyar ke fuskanta. Daga cikin kudaden da aka biya har da kashi 60% na albashin watan Satumba 2017 da aka dakatar, da kuma kudin alawus na kula da dalibai a shirin SIWES na tsawon zangon karatu biyar.

More from this stream

Recomended