Asisat: ‘Yar wasan Barcelona ta yi tsokaci kan Ramadana

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Yar kwallon Najeriya Asisat Oshoala da ke taka leda a Barcelona

Tauraruwar ‘yar kwallon Najeriya kuma ta ƙungiyar mata ta Barcelona, Asisat Oshoala ta bayyana abin da take ji game da kasancewar yau Juma’a a matsayin ranar azumin Ramadana 29.

Kamar yadda kuke gani, Oshoala ta wallafa a Twitter cewa: “Na 29….#Ramadan”.

Sai dai BBC ba ta iya fahimtar me ‘yar kwallon ke nufi ba; murna ce ko alhinin rabuwa da Ramadana.

Amma muna fatan ku za ku iya fahimta – musamman ma waɗanda korona ta haramta wa ganawa da abar ƙaunarsu ƙwallon ƙafa.

More from this stream

Recomended