
An yi wa Stephen fyade a 2011 lokacin rikicin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo
An fara wallafa shi a ranar 4 ga watanAgusta na 2017
“Idan na fadi abin da ya faru, mutane za su guje ni. Su kansu mutanen da suka yi min magani ba za su sake musabiha da ni ba.”
An yi wa Stephen Kigoma fyade lokacin da aka yi rikici a kasarsa, Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.
Ya bayyana wa wakilyar BBC Alice Muthengi halin da ya fada a ciki, yana mai yin kira ga mutanen da suka fuskanci wannan matsala su fito fili su bayyanawa duniya.
“Na boye cewa an yi min fyade. Ba zan iya fada ba – hakan tamkar sabo ne,” in ji shi.
“A matsayina na namiji ba zan iya kuka ba. Mutane za su ce ni matsoraci ne, rago, kuma shashasha.”
An yi wa Stephen fyade ne lokacin da wasu maza suka kai hari a garinsu Beni da ke arewa maso DR Congo.
“Sun kashe mahaifina. Mutum uku sun yi min fyade, sannan suka ce: ‘Kai namiji ne, yaya za ka ce an yi maka fyade?’
“Sun yi hakan ne domin ya zama wani makami da za su yi amfani da shi domin rufe min baki.”
- ‘Mutum 12 sun yi wa ‘yar shekara 12 fyade a Jigawa’
- Hukuncin ‘kisa ne kawai zai yi maganin fyaɗe a Najeriya’
Bayanya tsere daga Uganda a 2011, Stephen ya samu taimakon likitotic – bayan an duba an ga ceewa babu sauran raunuka a duburarsa.
An kai shi ya ga likitan da ke duba mutanen da aka yi wa fyade a lokutan yaki, kuma shi kadai ne namiji a cikin wadanda likitan ya gani.
“Na ji kamar na nutse a kasa don wulakanci. Na je kasar da ba tawa ba domin yi wa likita bayani kan abin da ya faru da ni. Abin da nake jin tsoron fada kenan.”
Hakkin mallakar hoto
AFP
An yi wa Stephen a asibitin Mulago, babban asibitin kwararru na Uganda
Stephen ya samu shawarwari kan yarda zai manta da abin da ya same shi ta hnyar kungiyar the Refugee Law Project,wacce ke birnin Kampala na kasar Uganda, inda shi da wasu mutum biyar suka yi bayani kan abin da ya same su.
Amma ba su kadai wannan lamari ya shafa ba.
Ba a kai wa ‘yan sanda korafi ba
Kungiyar The Refugee Law Project, wacce ta yi bincike kan yi wa maza fyade a DR Congo, ta wallafa rahoto kan yin lalata da ‘yan gudun hijirar Sudan ta kudu a arewacin Uganda.
Ta gano cewa fiye da kashi 20 cikin 100 na mata sun kai rahoton yi musu fyade – idan aka kwatanta da maza masu kashi hudu.
“Babban dalilin da ya sa maza kadan ke kai rahoton cin zarafinsu shi ne kada a mayar da su saniyar ware,” in ji Dr Chris Dolan, daraktan kungiyar, a hirarsa da shirin Focus on Africa na BBC.
Hakkin mallakar hoto
AFP
Uganda ta karbi ‘yan gudun hijira sosai a 2016 wadanda suka tserewa rikicin Sudan ta kudu
Ya kara da cewa ana fuskantar kalubalen wajen shari’a idan maza suka kai rahoton yi musu fyade.