Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta yi babban taronta inda wakilai suka amince da takarar Shugaba Muhammadu Buhari a yayin zaben da za a yi badi.
Shugaba Buhari shi kadai ne dan takara daya tilo da ya nemi jam’iyyar ta tsayar da shi takara a zaben na badi, inda yake neman wa’adi na biyu.
Wakilai dubu 7,000 ne suka taru domin amincewa da takarar ta Muhmmadu Buhai karo na biyu.
APC ta ce a zabukan da aka yi a jihohi a makwannnin da suka gabata, dan takarar ta su ya samu kuri’u miliyan 14,842,072.
A Kano ne Buhari ya samu kuri’u mafi yawa, da suka kai kusan miiliyan uku, sai kuma jihar Lagos da ya samu kuri’u miliyan biyu da dubu dari biyu.
Bayan ‘yan jam’iyyar sun nuna amincewa da takarar ta sa, shugaba Muhammadu Buhari shi ma ya yi jawabin amince wa da tsayar da shi takarar.
- Rikici ya kunno kai a PDP a Kano
- APC ta rushe shugabanninta na Zamfara
“‘Yan uwa na ‘yan jam’iyya, cikin kaskantar da kai na tsaya a gabanku a yau ina mai amince wa da tsayar da ni da jam’iyyar mu APC ta yi don yi mata takara a zaben shekarar 2019.”
Haka kuma Shugaba Buhai ya bayyana wasu nasarori da ya ce gwamnatinsa ta cimma tun bayan da ya karbi mulki a shekarar 2015.
Daga cikin wadanda suka halarci babban taron na APC har da wasu da suka sauya sheka daga PDP zuwa APC, kamar Dr. Jamil Isyaku Gwamna da ya nemi takarar gwamnan jihar Gombe a jam’iyyar PDP, amma ya fice daga jam’iyyar saboda zargin rashin adalci wajen zaben fitar da gwani.
Ya ce a ganin sa APC ta yi rawar gani a zbukan na ta.
To sai dai akwai rikice-rikice a jihohi da dama a jam’iyyar ta APC saboda wasu na zargin rashin adalci yayin zabukan.
PDP za ta san wanda zai kara da Buhari
Ita ma babbar jam’iyyar hamayya ta Najeriya PDP tana dab da sanin wanda zai yi mata takarar shugabancin kasar a zaben na badi.
Wakilan jam’iyyar sun shafe dare har zuwa asubahin Lahadi suna zabar wanda wanda zai kara da shugaba Buhari na APC a zabukan.
Mutum 12 ne ke neman PDP din ta ba su damar yin takarar.
PDP ta gudanar da na ta taron ne a birnin Fatakwal na jihar Rivers a kudu maso kudancin Najeriya.
A ranar Lahadin nan ne wa’adin da hukumar zaben Najeriya INEC ta debarwa jam’iyyu su mika sunayen ‘yan takara ya ke cika. Don haka dole ne jam’iyyun su kunshe sunyen kowaye su mika wa INEC don gudun kada wankin hula ya kai su dare
.