APC ta soke zaben zamfara a karo na biyu

Zaben fid da gwanin Zamfara


Yadda mutane suka fito a zaben fid da gwanin Zamfara

A Najeriya, kwamitin zaben fid da gwani na masu neman takarar gwamna a jam`iyyar APC ya soke zaben aka fara a jihar Zamfara sakamakon tabka magudi da tabarbarewar tsaro a lokacin zaben.

A jiya ne aka fara zaben bayan an yi ta turka-turkar kusan mako guda.

Gwamnatin jihar ta ce zaben bai soku ba, kuma za ta ci gaba da gudanar da shi.

Kwamitin zaben, wanda ya yi jawabi ga `yan jarida a hedikwatar `yan sandan jihar Zamfara, ya yi zargin cewa akwai matsaloli da dama wadanda suka jibanci magudi da tsaro da suka dabaibaye zabe, kuma babu abin da ya fi dacewa face soke shi.

A cewar shugaban kwamitin zaben Dr Abubakar Fari, ya ce akwai wasu ma’aikatan gwamnati da ma’aikatan zabe da suka karbe takardun zabe suka kuma cike sakamakon da suke so a sanar da mutane.

Dr Fari ya ce kananan hukumomin da aka samu irin wannan sun hada da Talata mafara da bakura da maradun da maru da bungudu da zurmi da birnin magaji sai kum Gusau.

  • Rikici ya barke a Zamfara kan zaben fid da gwani
  • ‘Zaben fidda gwani ba zai yiwu ba a Zamfara’

Shugaban kwamitin ya ce wadanan dalilai sun sanya an dage zaben sai abin da Allah ya yi, kuma hedikwatar jam`iyyar APC da ke Abuja ce kadai ke da hurumin tsayar da ranar da za a yi sabon zabe.

Amma, gwamnatin jihar Zamfara a nata bangaren, ta ce sam ba za ta sabu ba, inda ta zargin shugaban kwamitin da cewa dan-koren wasu daga cikin masu neman takarar ne, don haka ne ta yi fatali da matakin da kwamitin ya dauka na soke zaben.

Gwamnan jihar Abdula`ziz Yari ya ce zabe bai soku ba, hasali gwmnati za ta dora daga inda kwamitin zaben ya tsaya ba tare da bata lokaci ba.

Masu neman takara na cikin wadanda suka jikkata a je-ka-ka-dawon da aka yi ta yi sakamakon daddage zaben.

Masassharar da ke damun zaben fid da gwanin jihar Zamfara dai za a iya cewa ta ki jin magani, musamman ma idan aka yi la`akari da cewa an so a yi zaben da takardun kada kuri`a abin ya gagara, kana aka jarraba `yar tinke ga shi ita ma ta haifar da tankiya, wadda a karshe an yi rabuwar da ba rakiya tsakanin bangaren gwamnatin jihar da `yan kwamitin zaben.

More from this stream

Recomended