APC ta rushe shugabanninta na Zamfara

Adams Oshimole


Kwamitin koli na jam’iyyar APC ya kuma hana gwamnan jihar Abdulaziz Yari sanya hannu a harkokin zaben

Kwamitin koli na jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ya hana gwamnan jihar Abdulaziz Abubakar Yari sake tsoma hannu kan zaben fitar da gwani na ‘masu neman takara a jihar.

Haka kuma kwamitin ya rushe shugabannin jam’iyyar ta APC na kowane mataki a jihar ta Zamfara.

Wata sanarwa da uwar jam’iyyar ta fitar dauke da sa hannun mukaddashin kakakinta Mista Yakini Nabena, ta ce a yanzu kwamitin da uwar jam’iyyar ta nada shi ne zai gudanar da zabukan fitar da gwani a jihar.

Kawo yanzu gwamnatin jihar ta Zamfara da shugabannin da aka rushe ba su mayar da martani kan matakin ba.

Zabukan da kwamitin zai gudanar sun hada da na masu neman takarar gwamna, da na ‘yan majalisu a jihar.

Sanarwar ta ce za a gudanar da zabukan na fitar da gwani na gwamna da na ‘yan majalisa ranar Asabar da Lahadi.

A wannan makon dai an samu sabani da mummunar takaddama kan zabukan fitar da gwamnati, lamarin da ya kai ga tashe-tashen hankula.

Wasu rahotannin ma na cewa an samu asarar rayuka.

An shafe wannan makon ana sanya ranar zaben ana soke wa, saboda sabanin da ake fuskanta tsakanin gwamnan jihar da kuma kwamitin gudanar da zaben da uwar jam’iyyar ta tura Zamfara.

More from this stream

Recomended