APC ta lashe zaben kujerun ƙananan hukumomi da kansilolin jihar Kaduna

Jam’iyyar APC ta lashe zaben dukkanin kujerun ƙananan hukumomin jihar Kaduna 23 da kuma na kejerun kansilolin jihar.

Hajara Muhammad shugabar hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kaduna ce ta sanar da sakamakon zaɓen.

Ta sanar da cewa biyo bayan tattara sakamakon zaɓen da jami’an tattara sakamako suka sanar a matakin ƙananan hukumomi 23  da kuma mazaɓu 255  kamar yadda doka ta tanadar saboda da haka ta sanar da cewa jam’iyar APC ta lashe zaben a kananan hukumomi 23 da kuma dukkanin mazaɓun jihar 255.

Tun da farko gwamnan jihar, Mallam Uba Sani ya bayyana gamsuwarsa kan yadda zaɓen yake gudana a faɗin jihar.

Sani ya bayyana haka ne lokacin da yake kaɗa kuri’arsa a akwatu na 047 dake Kawo.

More News

Tinubu ya dawo gida Najeriya daga Birtaniya

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo gida Najeriya bayan da ya shafe mako biyu yana hutu a Birtaniya. Shugaban ƙasar ya sauka a filin...

An sallami ƴan sanda uku daga bakin aiki kan kisan wani dalibi

Rundunar ƴan sandan jihar Kwara ta ce ta sallami jami'an ta uku da aka samu suna da hannu a kisan wani dalibin makarantar kimiya...

Ribadu ya koka kan yadda jami’an tsaro suke sayarwa da ƴan ta’adda bindigogi

Mai bawa shugaban shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya ce wasu daga jami'an ƴan sanda da kuma sojoji suna ɗaukar bindigogi daga...

Gwamnan Legas Sanwo-Olu ya kara mafi ƙarancin albashi zuwa naira 85,000

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana shirin gwamnatinsa na fara biyan sabon mafi karancin albashi na N85,000 ga ma'aikatan jihar.Sanwo-Olu ya bayyana hakan...