APC ta lashe zaben dan majalisa a Kogi

[ad_1]

Voters line up to cast their ballots in an election in Nigeria

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Hukumar zabe ta Najeriya INEC ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC mai mulkin kasar a matsayin wanda ya lashe zaben da ya gudana a jiya Asabar.

Farfesa Rotimi Ajayi na sashin nazarin kimiyyar siyasa na Jami’ar gwamnatin Tarayya ta Lokoja ne ya bayyana sakamakon.

Ya bayyana Haruna Isa na dan jam’iyyar APC, wanda ya sami kuri’u 26,860 a matsayin wanda ya lashe zaben:

“Haruna Isa ya cika dukkan sharuddan zabe, kuma hi ne ya sami kuri’u mafi yawa, saboda haka shi ne ya lashe zaben dan majalisar da ya gudana.”

An gudanar da zaben ne don maye gurbin dan majalisar wakilai na mazabar Lokoja/Kogi Koton-Karfe wanda wata babbar kotu ta sauke daga mukamin.

Dan takarar APCn ya fafata ne da wasu ‘yan takara su takwas daga jam’iyyu daban-daban.

Mai bi masa shi ne Abubakar B. Muhammad na jam’iyyar PDP wanda ya sami kuri’u 14,845.

Sai kuma Muhammad Kazeem na jam’iyyar ADC wanda shi kuma ya sami kuri’u 2,984.

PDP ta lashe zaben Kuros Riba

A jihar Kuros Riba ma an gudanar da zaben cike gurbi a mazabar gundumar Obudu.

Dan takarar jam’iyyar PDP Abbey Awara Ukpukpen ne lashe zaben da kuri’u 12, 712.

Ya doke sauran ‘yan takarar da suka fafata da shi, ciki har da na jam’iyyar APC wanda ya sami kuri’u 4,345.

An dai gudanar da zabuka guda hudu na maye gurbi a wasu mazabu dake ciki tarayyar Najeriya a jiya Asabar.

Mazabun sune na sanatoci a Arewacin Katsina da Kudancin Bauchi da na dan majalisar wakilai a mazabar Lokoja/Kogi Koton-Karfe na jihar Kogi, da kuma na dan majalisar jiha a Kuros Riba.

[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...