APC ta lashe zaɓen dukkanin shugabannin ƙananan hukumomin jihar Ekiti

Jam’iyar APC ta lashe dukkanin zaɓen shugabannin kananan hukumomin jihar Ekiti da kuma na kujerun kansiloli 177 da aka gudanar.

A ranar Asabar ne hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Ekiti ta gudanar da zaɓe a dukkanin ƙananan hukumomin jihar.

A cewar kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN jami’an tattara sakamakon zaben sune suka gabatar da sakamakon a hedikwatar hukumar dake Ado-Ekiti.

A ranar Lahadi ne shugaban hukumar, Cornelius Akintayo ya yabawa masu kada kuri’a kan yadda aka gudanar da zaɓen lafiya.

Related Articles