
Jam’iyar APC ta lashe kujerun ciyamomi 20 na kananan hukumomin jihar Ribas a zaben jihar da aka gudanar.
Hukumar zabe mai zaman kanta jihar RSIEC ce ta gudanar da zaben ƙarƙashin sanya idanun gwamnan riko na jihar Ibok-Ete Ibas.ffw
Ita ma jam’iyar adawa ta PDP ta samu nasarar lashe zaben kujerun ciyamomi na kananan hukumomi 3.
Michael Ekpai, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar ne ya sanar da sakamakon zaɓen a ranar Lahadi.
Siminalayi Fubara gwamnan jihar ya yi rashin nasara a ƙaramar hukumarsa ta Opobo-Nkoro inda jam’iyar PDP ta lashe zaben kujerar shugaban karamar hukumar.
Fubara da magoya bayansa sun kauracewa wurin zaɓen na ranar Asabar.
Jim kadan baya kada kuri’asa ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ce yanzu lokaci ya yi da ya kamata a janye dokar ta ɓaci da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya saka jihar.