Kwamitin riko dake jagorancin Jam’iyar APC na kasa ya kaddamar da shugabbin jam’iyar daga jihohi 34 da kuma birnin tarayya Abuja gabanin babban taron jam’iyar na ranar 26 ga watan Faburairu .
Amma kuma jam’iyar ta cire Kano da Sokoto daga jerin jihohin da aka rantsar da shugabanninsu.
Wadanda aka kaddamar sun hada da Kingsley Ononogbu (Abia); Ibrahim Bilal (Adamawa); Augustine Enefiok Ekanem (Akwa Ibom); Basil Ejike (Anambra); Babayo Aliyu Misau (Bauchi); Dennis Otiotio (Bayelsa); Augustine Agada (Benue); Ali Bukar Dalori (Borno) da; Alphonsus Orgar Eba (Cross River).
Sauran su ne Omeni Sabotie (Delta); Stanley Okoro Emegha (Ebonyi); David Imuse (Edo); Omotosho Paul Ayodele (Ekiti); Ogochukwu Agballah (Enugu); Nitte K Amangal (Gombe); Macdonald Ebere (Imo); Aminu Sani Gumel (Jigawa); Emmanuel Jekada (Kaduna); Muhammed Sani (Katsina), Abubakar Muhammed Kana (Kebbi) da kuma; Abdullahi Bello (Kogi).
Ragowar sun hada da Sunday Adeniran Fagbemi (Kwara); Cornelius Ojelabi (Lagos); John D Mamman (Nasarawa); Haliru Zakari Jikantoro (Niger); Yemi Sanusi (Ogun); Ade Adetimehin (Ondo); Adegboyega Famodun (Osun); Isaac Omodewu (Oyo); Rufus Bature (Plateau); Emeka Bekee (Rivers); Ibrahim Tukur El-Sudi (Taraba); Muhammed A. Gadaka (Yobe); Tukur Umar Danfulani (Zamfara) and; Abdulmalik Usman (FCT).