
Jam’iyar APC mai mulki ta zabi sanata Ovie omo-Agege daga jihar Delta a matsayin wanda take so ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawa.
Tunda fari jam’iyar ta goyi bayan sanata Ahmed Lawal daga jihar Yobe a matsayin wanda take so ya zama shugaban majalisar dattawa.
Har ila yau jam’iyar ta kuma zabi Idris Wase daga jihar Plateau a matsayin wanda zai zama mataimakin shugaban majalisar wakilai.
A wata sanarwa mai magana da yawun jam’iyar Lanre Issa-Onilu ya ce jam’iyar ta cimma wannan matsaya ne bayan data tuntubi bangarori daban-daban.
Jam’iyar ta umarci dukkanin ƴaƴanta dake majalisun biyu da su goyi bayan mutanen da ta tsayar a zaben da za a gudanar gobe.
A gobe Laraba ne majalisun biyu za su gudanar da zamansu na farko.