APC ta amince da tsarin zaben ‘yan takarar gwamna

Shugaban jam'iyyar APC Adams Oshiomhole da manema labarai

Hakkin mallakar hoto
Getty Image


Jam’iyyar ta APC ta amince da tsarin da kowa ce jiha ta gabatar mata tana son bi wajen fitar da dan takarar gwamna

Kwamitin gudanarwa na kasa na jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ya amince da tsarin zaben fitar da gwani na ‘yan takarar gwamna da za a yi ranar Asabar, 29 ga watan Satumba a jihohin kasar 36.

Tsarin dai ya kasu kashi biyu ne, na zabe kai tsaye, wanda ake kira kato bayan kato da kuma wanda ba na kai tsaye ba wato wanda wakilai ne wadanda ake kira deleget (delegates) za su yi.

Sai dai kuma a wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar mai dauke da sa hannun mukaddashin sakatarenta na watsa labarai, Mista Yekini Nabena, ta ce kwamitin na kasa ya haramta wa ‘yan kwamitin gudanarwa na jihar Adamawa yin zaben dantakarar gwamnan jihar walau a matsayin wakilai (deleget) ko kuma masu sanya ido a zaben.

An yi musu wannan haramcin ne saboda kamar yadda kwamitin na kasa ya ce sun karkata ga bangaren wani daga cikin masu neman takarar.

Ga jerin yadda kowa ce jiha ta zabi tsarin da za ta bi wajen fitar da ‘yan takarar wanda kuma kwamitin tarayyar ya amince:

Zaben kai tsayeZaben Deleget

1- ABIA 1- ADAMAWA

2- AKWA IBOM 2- BENUE

3- ANAMBRA 3- BORNO

4- BAUCHI 4- DELTA

5- BAYELSA 5- EBONYI

6- CROSSRIVER 6- ENUGU

7- EDO 7- GOMBE

8- EKITI 8- JIGAWA

9- IMO 9- KADUNA

10- KANO 10- KASTINA

11- LAGOS 11- KEBBI

12- NIGER 12- KOGI

13- OGUN 13- KWARA

14- ONDO 14- NASARAWA

15- OSUN 15- OYO

16- TARABA 16- PLATEAU

17- ZAMFARA 17- RIVERS

18- SOKOTO

19- YOBE


Ana ganin zabukan fitar da ‘yan takara kalubale ne ga jam’iyyu a Najeriya

More from this stream

Recomended