Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya na gudanar da zaben fitar da ‘yan takara na gwamnonin jihohi.
APC na gudanar da zaben ne ranar Lahadi a sassan jihohin Najeriya domin tsayar da ‘yan takarar gwamna.
Sai dai kuma uwar jam’iyyar ta dage zaben fitar da ‘yan takarar gwamnan jihohin Legas da Imo zuwa ranar Litinin saboda wasu dalilai da ba ta bayyana ba.
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ma na gudanar da zaben fitar da ‘yan takarar gwamnonin ne a daidai lokacin da APC ke nata zaben.
PDP ta fitar da wata sanarwar inda ta musanta jita-jitar da aka yada kan cewa ta dage zaben fidda gwani na gwamnoni da ta shirya gudanarwa a ranar Lahadi
PDP ta sanar da dukkan wakilanta, da ‘ya’yan jam’iyyar da wadanda suke son tsayawa takara cewa babu wani sauyi da aka samu.
Sai dai sanarwar da sakataren yada labaran Jam’iyyar ya fitar ta ce zaben bai shafi jihohin Kano da Imo da kuma Lagos ba, tana mai cewa za a sanar da ranar da za a gudanar da nasu zaben.
Tsarin zaben APC dai ya kasu kashi biyu ne, inda a wasu jihohi za a bi tsarin zabe na kai-tsaye, wanda ake kira kato bayan kato.
Wasu jihohin kuma za su yi amfani da tsarin wakilai ne wanda ake kira na deleget.
Akwai dai jihohi da dama da jam’iyyar APC ke fuskantar baraka saboda gwagwarmayar neman takarar kujerar gwamnan.
A jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, wasu masu neman tsayawa takarar gwamna a karkashin jam`iyyar APC sun yi barazanar kauracewa zaben saboda suna ganin ba za a yi masu adalci ba.
Wasu daga cikin masu neman takarar na zargin cewa an boye `yan kwamitin zaben da nufin tabka magudi a zaben, don haka za su kaurace masa.
Za a yi amfani da tsarin zabe na kato bayan kato domin fitar da dan takara a Zamfara.
Jihar Bauchi ma na daya daga cikin jihohin da ake takaddama inda ‘yan takara uku ke hamayya da gwamnan jihar Muhammadu Abdullahi Abubakar wanda neman wa’adin shugabanci na biyu.
A jihar Gombe da APC ke adawa kusan mutane tara ke neman takarar kujerar gwamna, kuma kowannensu na ganin shi ya fi cancanta.
Jihar Borno ce ta fi yawan ‘yan takarar gwamna inda akalla ‘yan takara 21 ne ke neman kujerar gwamna a jihar daya daga cikin jihohin arewa maso gabashi da ke fama da rikicin Boko Haram.
Duk wanda ya yi nasara daga cikin ‘yan takarkarin, ana has ashen shi zai gaji Kashim Shittima wanda ke kamala wa’adin mulkinsa na biyu.
Jihar Borno za ta yi amfani da tsarin deleget wajen zaben dan takarar gwamna maimakon tsarin kato bayan kato.
Masharhanta siyasar jihar dai na ganin akwai yiyuwar yawancin ‘yan takarar za su janye domin marawa wanda ake ganin gwamna Kashim Shettima ke goyon baya.
A jajibirin zaben, shugabancin uwar jam’iyyar na kasa ya fitar da jerin sunayen kwamitin da za su jagoranci zaben fitar da ‘yan takarar gwamnonin a jihohi.