APC ba ta yi adalci ba a zabukan fitar da gwani — Aisha Buhari

Aisha Buhari

Uwar gidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta soki jam’iyya mai mulki APC dangane da yadda ta gudanar da zabukan fitar da gwaninta a 2018.

Aisha Buhari, wadda ta rubuta a shafinta na Instagram cewa ‘ Abin takaici ne wasu ‘yan takara sun yi amfanin da kudin guminsu sun sayi fom din takara, sannan an tantance su, kana sun yi yakin neman zabe iya karfinsu, amma kuma an cire sunayensu a ranar zabe.’

Uwargidan shugaban Najeriyar, ta ce ‘ Babban abin takaicin shi ne yadda wadannan ‘yan takara suka sayi fom din a kan kudi mai yawa’.

Ta ce ‘ Da yawa daga cikin wasu ‘yan takarar kuma har yanzu suna dakon sakamakon zaben, wanda sanin kowa ne cewa tuni aka ba wa wasu takarar shi yasa ake jan kafa wajen fadin sakamakon.’

Aisha Buhari ta ce, Makasudin kafa jam’iyyar APC shi ne don a samar da sauyi nagari, amma bain ttakaicin shi ne yadda wannan al’amari ya faru a karkashin jagorancin Adams oshimole, mutumin da aka sani da nuna damuwa da kuma kokarin kwatowa talakawa ‘yancinsu.

Uwargidan shugaban Najeriyar ta ce, wannan al”amari ya sa mutum ba shi da zabi illa ya nesantar da kansa daga wannan rashin adalcin ya kuma yi magana a madadin wadanda aka tauye musu hakkinsu.

Ta ce yana da muhimmanci al’umma su tashi tsaye wajen ganin cewa ba a tauye musu hakkinsu ba.

More News

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...

Mutane 18 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota

Aƙalla fasinjoji 18 ne suka ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Ojebu-Ode zuwa Ore a yankin Ogbere dake...

AMBALIYA: Bafarawa ya ba wa al’ummar Sokoto gudunmawar naira biliyan 1

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya bayar da gudummawar Naira biliyan daya ga al’ummar Sokoto, domin rage radadin wannan annoba.An bayyana hakan...

Ƴanbindiga sun kai hari coci-coci a Kaduna, sun kuma yi garkuwa da mutane

Mutane 3 ne ake fargabar sun mutu, sannan an yi garkuwa da wasu 30 bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a...