Tsohon mai ba Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin siyasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ba jam’iyyar talakawa ba ce, illa jam’iyyar masu riƙe da muƙamai.
Baba-Ahmed ya faɗi haka ne a ranar Talata yayin wata hira a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels.
A cewarsa, mutane da dama na kuskuren tunanin cewa kasancewar APC tana mulki a yawancin jihohi na nufin ta mallaki ƙasar gaba ɗaya. Ya ce hakan ba gaskiya ba ne, yana mai jaddada cewa yawancin gwamnonin jihohi, sanatoci da ‘yan Majalisar Wakilai sun sauya sheƙa ne daga jam’iyyunsu zuwa APC.
Baba-Ahmed ya ƙara da cewa akwai bambanci a bayyane tsakanin jam’iyyar da ke da iko da kuma jam’iyyar da ke wakiltar muradun al’umma.
APC Ba Jam’iyyar Talakawa Ba Ce – Hakeem Baba-Ahmed

