An samu ɓarkewar annobar cutar kwalara a ƙaramar hukumar Kirikasamma da kewayenta a jihar Jigawa.
Kawo yanzu mutane 7 aka tabbatar da mutuwarsu sanadiyar annobar a yayin a wasu da dama ke can kwance a asibiti inda suke karbar magani.
Jami’in tsare-tsare na hukumar kula da lafiya a matakin farko na ƙaramar hukumar Kirikasamma, Musa Abdullahi Digadige ya ce ɓarkewar annobar cutar ta shafi ƙauyuka da dama da suka haɗa da Malori, Maikintari, Dilmari, Kirikasamma, da kuma wani sashe na na ƙauyen Baturiya.
A cewar Digadige alamomin cutar sun haɗa da gudawa, ƙullewar ciki, jin yin amai, amai da kuma zazzaɓi.
Shugaban Sashen Ruwa da Tsafta, Muhammad Maisamari ya ce an tura tawagar jami’an kiwon lafiya ya zuwa yankunan da abun ya shafa domin su bayar da kulawar da ta kamata.
Ƙaramar hukumar ta kuma sayo magunguna da sauran kayayyakin da suka kamata domin samun nasarar maganin cutar.
Daraktan mulki da gudanarwa na ƙaramar hukumar, Idris Gambo Abubakar ya yi alƙawarin bayar da dukkanin taimakon da ya dace domin daƙile yaɗuwar cutar.
Hukumomi sun alaƙanta ɓarkewar cutar da gurɓatar ruwan sha sanadiyar ambaliyar ruwa da aka samu a yankin sanadiyyar mamakon ruwan sama.