Akalla mutane 12 ne suka mutu, yayin da wasu sama da 230 ke karbar magani a asibitoci daban-daban, sakamakon barkewar cutar kwalara da ta bulla a Jihar Neja.
Rahotanni sun bayyana cewa cutar ta fara bayyana ne a karshen mako, musamman a karamar hukumar Shiroro, kafin daga bisani ta yadu zuwa wasu kananan hukumomi shida.
Kananan hukumomin da suka fi fuskantar barazanar cutar sun hada da Minna, Bosso, Shiroro, Magama, Bisa da Munya, in ji hukumomin lafiya.
Kimanin mutum 239 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a yankunan da abin ya shafa, kuma dukkansu na samun kulawa a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da aka tanada a wadannan yankuna.
Gwamnatin jihar, a matsayin martani, ta bude cibiyar killace masu cutar a tsohon bangaren Asibitin Koyarwa na marigayi Sanata Idris Kuta da ke Minna.
Kwamishinan Lafiya ta Farko a jihar, Dakta Ibrahim Dangana, ya tabbatar da cewa an tura tawagar kwararru daga fannoni daban-daban domin dakile yaduwar cutar.
“A halin yanzu mun kafa cibiyoyin killacewa da warkarwa a kowace karamar hukumar da cutar ta bulla, domin hana ta yaduwa,” in ji Dangana.
Ya ce ana gudanar da gagarumar wayar da kai ga jama’a, musamman ta hanyar hada kai da kungiyoyin addini irin su kungiyar Kiristoci ta CAN da kungiyoyin Musulunci, da kuma masarautu takwas da ke fadin jihar.
Dangana ya yaba da saurin daukar matakin da Gwamna Mohammed Bago ya yi, tare da jinjinawa kungiyoyin bada tallafi kan hadin kai da goyon bayan da suka bayar.
Haka zalika, Daraktan Lafiya ta Jama’a a Ma’aikatar Lafiya ta manyan asibitoci, Dakta Ibrahim Idris, ya bayyana cewa yankunan Chanchaga, Minna, Bosso da Shiroro su ne mafi muni wajen yaduwar cutar.
Gwamnatin jihar ta bukaci al’ummar Neja da su ci gaba da kiyaye ka’idojin tsaftar muhalli da kuma neman kulawar likita da zarar an fara alamomin cutar, domin rage yaduwarta da kuma kare rayuka.
Annobar Cutar Kwalara Ta Kashe Mutane 12 a Jihar Neja, Sama da 230 Na Kwance a Asibiti
