Annobar Coronavirus: Shin lalaci a jinin dan Adam yake?

Five young adults sit on the floor in thought

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Being inactive might not come as naturally to us as we think

Watakila kuna cikin mutanen duniya sama da miliyan uku da suka kalli fim din da ofishin gwamnan California ya fitar. Bidiyon ya karade shafukan sada zumunta.

A hoton bidiyon, fitaccen mai barkwancin nan Larry David ya yi amfani da salon barkwancinsa wurin fadakar da mutane da jan hankalinsu su bi shawarwari mahukunta su zauna a gida don hana yada Covid-19.

Me ke damunku ne ”marasa wayo”, a cewarsa, an fa baku damar zama a gida kamar sarakuna, ku wuni gaban Talabijin!

Mun sha jin gargadin masana da ke cewa mu yi abubuwan da lokaci baya bamu damar aiwatarwa: mu motsa jiki, mu ninka yawan kayan marmari da gayenyakin da muke ci kamar sau 5 zuwa 10.

Da fari, shawarwari sun kasance kamar masu sauki; ku zauna a gida ku huta ku yi amfani da damarku.

Sai dai fa da alama abin ba sauki domin sabo da zaman gida ya soma haifar da gajiya kuma.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Shin da gaske ne cewa mutane sun fi son komai ya zo musu cikin sauki, babu batun juriya, komai so ake a samu cikin sauki.

Idan kuna da linzamin sauya tasha a hannunku me zai sa ku tashi kuna kokarin kashe talabijin? Idan kana da mota me zai sa ka tafi cefane a kan keke? Idan zaka samu ragin aikinka me zai sa ka damu kan yawan aikin da abokin aikin kake yi?

Duk wani salon aiki ko kokari na aiki ne da lafiyar kwakwalwa da ta jiki, don haka ba abin mamaki ba ne idan an samu bijirewa. Wasu lokutan kuma hakan dabi’unmu suke.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Ka taba mafarkin tsintar kanka baka aikin komai? Shingide a hannun kujera wuni guda. Kana kallon rufin gida ka tsunduma cikin dogon nazari.

Watakil wani ya kwadaitu da jin hakan, wasu lokutan kuma za ka ji baka bukatar komai – kawai bacci za ka sha ka more.

A wani bincike da aka gudanar shekaru da dama a Jami’ar virginia, mutanen da aka gwada nazari a kansu kowanne an barshi ya zauna cikin gida shi kadai ba tare da wani abin da zai dauke musu hankali ba.

An hana su waya, babu litattafai, babu abin kallo – kuma ba a amince su don shingida wato baccin gajeren lokaci. An makala wata na’ura a kafarsu sannan aka bar su na tsawon minti 15.

Wata dama ce ta hutawa na wani gajeren lokaci ba tare da wani abu da zai dauke ko hanasu hutun ba.

To me aka cimma?

Kafin a bar mutum shi kadai, an koyawa mutanen yadda ake latsa wasu madanai na kamfuta wanda aka hada da na’urar da aka makala a jikinsu.

Na’urar dai na jan su idan sun dana kamfutar.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Zama kadaici akwai wuya

Kashi 71 cikin 100 na maza da kashi 25 cikin 100 na mata kamfutar ta ja su lokacin da suke cikin kadaici – wani mutum cikinsu sau 190 na’urar ta ja shi.

Hakan ya nuna cewa zama ba ka taba komai abu ne mai wahala, kuma mutanen da yi wannan gwaji da su sun yi kokarin ganin sun cimma hakan.

A wasu lokutan mutane na son bin hanyar sauki, sai dai a wasu lokutan hakan nasa mu san darajar ko amfani da kake yi wa kanka.

Wannan gwaji misali ne, amma mun san cewa a akasarin lokuta na rayuwa mutane nayi abubuwa da ba wajibi ba ne a rayuwarsu ko wanda ba a bukata a lokacin.

Idan ka yi tunanin abokanka da ke atisaye ko tsere gudu za aka fahimci yanayin lafiyarsu.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wasu mutanen ba sa wasa da batun motsa jikinsu

To ina batun mutane da ke zagaye wurare da dama suna taka sayyadarsu ko cikin jirgin ruwa?

Michael Inzlicht na Jami’ar Toronto ya ce wannan wani hubbasa ne da ba kasaifai kowa ke iya shi ba.

A wasu lokutan muna daukan abin da sauki, amma kuma hakan ya taimaka mana wajen sanin mizaninmu.

Muna koyon rayuwa ne tun da wuri. A lokutan da muke yara duk wani kokari ko tarbiyar da aka gina mu a kansu na taimakawa.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

A wannan zamanin mutane da dama basa wahala wajen hawa tsauni

Ana iya hawan tsauninka da dama yanzu a duniya duk tsayinsa ta hanyoyin da zamani ya tanadar.

Masu zuwa yawon bude ido da sha’awar hawa tsauninka yanzu haka komai yazo musu cikin sauki.

Yayin da muke zaman gida ko zaman killace kai, kwance akan kujera kana kallon talabijin na nuna yadda muke rage lokaci don samun sauki ko huce gajiya.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mutane da dama na son hutu ta hanyar latsa waya

More News

Zanga-zanga: An jibge Æ´an sanda 4200 a Abuja

Rundunar Æ´an sandan birnin tarayya Abuja ta tura Æ´an sanda 4200 gabanin zanga-zangar da za a gudanar a cikin watan Agusta. Kamar yadda masu shirya...

Kamfanin NNPC ya shirya daukar karin ma’aikata

Kamfanin mai na Nigerian National Petroleum Company Limited ya shirya daukar karin ma’aikata.Kakakin kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya tabbatar da hakan a wata...

Ya kamata matasa su yi haÆ™uri zanga-zanga ba ita ce mafita ba – Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli ya ce matasa su ƙara haƙuri da gwamnatin tarayya su janye zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a...

Zanga-zanga: Tinubu ya gana da gwamnonin APC

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyar APC. Taron ganawar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa ta...