Anne Chidzira Muluzi: ‘Yan Malawi na alhinin mutuwar matar tsohon shugaban kasar

  • Daga Peter Jegwa
  • Lilongwe, Malawi

Asalin hoton, Twitter/ SKChilima

Bayanan hoto,
Shugaban kasa mai ci ya bayyana Anne Chidzira Muluzi a matsayin “mai mutunci, da kulawa da taimakon jama’a”

Mace ta farko da ta fara rike matsayin “first lady” wato uwargidan shugaba kasa a Malawi ta mutu tana da shekara 69.

Anne Chidzira Muluzi, wacce ake mutuntawa sosai a kasar Malawi, ta mutu ne sakamakon cutar daji a wani asibiti mai zaman kansa a kasar Kenya.

Ta karbi mukamin uwargidan shugaban kasa bayan da aka zabi mijinta Bakili Muluzi a matsayin shugaban kasa a shekara ta 1994 lokacin da aka kawo karshen mulki mai jam’iya daya.

Wanda ya gada tun bayan samun ‘yancin kai, Hastings Kamuzu Banda, bai taba yin aure ba.

Mista Banda ya yi zaman dadiro ne da sakatariyarsa Cecilia Kadzamira, wacce ya bai wa matsayin “uwargida a hukumance”.

Shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera ya ce ya “kadu matuka” da samun labarin mutuwar matar tsohon shugaban kasar.

“‘Yan kasar Malawi za su rika tunawa da Madame Chidzira Muluzi a matsayin mai mutunci, da kulawa, da kaunar jama’a wacce ta bauta wa wannan kasa tukuru,” ya ce.

A sakon ta’ziyyarsa, mataimakin shugaban kasar Saulos Klaus Chilima ya bayyana cewa ta tallafa wa “dubban mabukata da kananan yara da ke fusantar matsaloli” ta hanyar gidauniyarta ta Freedom Foundation Trust.

Ya kara bayyanawa cewa “zuciya mai kyau ta daina bugawa, mutuwa ta dauke mace mai kirki”.

Har yanzu gwamnati ba ta sanar da lokacin da za a gudanar da jana’izarta da kuma lokacin da za a kawo gawarta gida daga kasar Kenya ba.

Mrs Muluzi ta mutu ta bar da daya, Atupele Muluzi, wanda shi ne shugaban jam’iyar adawa ta United Democratic Front (UDF).

Sun rabu da mijinta a shekarar 1999. Ya zama shugaban kasa har ya zuwa shekarar 2004.

More News

Zanga-zanga: An jibge ƴan sanda 4200 a Abuja

Rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja ta tura ƴan sanda 4200 gabanin zanga-zangar da za a gudanar a cikin watan Agusta. Kamar yadda masu shirya...

Kamfanin NNPC ya shirya daukar karin ma’aikata

Kamfanin mai na Nigerian National Petroleum Company Limited ya shirya daukar karin ma’aikata.Kakakin kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya tabbatar da hakan a wata...

Ya kamata matasa su yi haƙuri zanga-zanga ba ita ce mafita ba – Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Nuhu Bamalli ya ce matasa su ƙara haƙuri da gwamnatin tarayya su janye zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a...

Zanga-zanga: Tinubu ya gana da gwamnonin APC

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyar APC. Taron ganawar da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa ta...