Ana zargin matashi da kashe mahaifiyarsa da ƴar’uwarsa

Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta tabbatar da cafke wani matashi da ake zargin ya kashe mahaifiyarsa, Misis Charity Orji da ‘yar uwar sa, Miss Ukamaka Orji, tare da binne su a wani kabari mara zurfi a bayan gidansu a jihar.

Wanda ake zargin mai suna Somadina Orji daga Igboariam a jihar Anambra, an ce ya aikata laifin ne a ranar Litinin, 4 ga watan Disamba, 2023, a Umuagu Inyi, a karamar hukumar Oji ta jihar Enugu.

Rahotanni da faifan bidiyo daban-daban na faruwar lamarin sun bayyana cewa, marigayiya Charity ‘yar asalin garin Inyi ce amma ta yi aure a Igboariam da ke jihar Anambra, ta shafe wasu shekaru tana zaune a gidansu da ‘ya’yanta.

Sai kuma ga shi danta wanda ake zargin yana ta’ammali da miyagun kwayoyi kuma ya dade yana fama da ita ya kashe ta.

More from this stream

Recomended