Ana zargin ƴan ƙungiyar asiri da hallaka Sarkin Hausawan Edo

‘Yan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne sun harbe wani mai suna Danladi, ɗaya daga cikin ‘ya’yan Serikin Hausawa a Birnin Benin, babban birnin jihar Edo.

Marigayi Danladi ya kasance yana shirin yin aure a watan Disamba kafin a kashe shi.

An rawaito cewa an kashe marigayin ne a shagon wani abokinsa da ke da nisan kimanin mita 100 daga yankin ‘yan sanda na Esigie a ƙaramar hukumar Oredo a jihar Edo.

Wata majiya da ya nemi a sakaye sunanta ta bayyana cewa, Danladi na zaune a shagon abokinsa a kan titin Enohuwa lokacin da ‘yan bindigar suka fito daga cikin mota GLK Benz suka harbe shi sau biyu daga kusa.

Majiyar ta bayyana marigayi Danladi a matsayin mutum mai sauƙin hali, “Shi ɗan Serikin Hausawa ne a wannan yankin. Mutuwar Danladi ta haifar da babban gibi a cikin iyalinsa kuma babban rashi ne ga matar da zai aura.”

More from this stream

Recomended