Ana rikici tsakanin Firaminista da Shugaban kasa

Masu zanga-zangar kin jinin gwamnati

Hakkin mallakar hoto
Reuters

—BBC Hausa

Image caption

Kungiyar Tarayyar Turai ta nuna bacin rai kan yadda masu zanga-zangar kin jinin gwamnati ke tayar da hankali

Kan shugabannin kasar Albaniya ya rabu a kan zaben kananan hukumomi da za a yi a karshen makon nan, lamarin da ya kara rura wutar dambarwar siyasar kasar.

Yayin da Shugaban kasar Ilir Meta ya bayar da umarnin a dage zaben har zuwa watan Oktoba, shi kuwa Firaminista Edi Rama kekasa kasa ya yi ya ki amincewa da dagawar, ya ce lalle sai ya gudanar da zaben kamar yadda aka tsara tun farko.

Daman tuni ‘yan jam’iyyun hamayya sun kaurace wa zaman majalisa, inda suka shafe watanni suna zanga-zangar kin jinin gwamnati.

Kauracewar da suka yi wa zaben kananan hukumomin ta tilasta matsar da zaben shugaban kasar, kamar yadda Mista Meta ya ce zanga-zangar ta hamayya da gwamnati da kauracewar ‘yan hamayya, ba za su sa a samu zaben ya kasance cikin gaskiya da adalci ba.

Sai dai Firaministan ya dage, inda ya tsaya kai da fata kan matsayarsa, ya ki amincewa da dagewar, dadin dadawa ma har ya dauki matakin fara shirin tsige Mista Meta.

Shi kuwa Shugaban ko gezau, sai ma ya sanya lokacin zaben zuwa ranar 13 ga watan Oktoba a yanzu, duk da cewa gwamnati da hukumar zabe sun kafe cewa ranar Lahadin nan za a fara zaben.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

A baya Albania ta nuna bukatarta ta shiga kungiyar Tarayyar Turai

Wannan kuma ya sa jagororin ‘yan hamayya suka lashi takobin daukar matakin hana yin zaben.

‘Yan hamayyar sun zargi Firaminista da shirin yin magudi da kuma almundahana, wanda a kan haka tun da farko suka bukaci a yi zabe na wuri.

Haka kuma suna son ganin an kafa gwamnatin rikon-kwarya, inda suka ki zaman tattaunawa domin samun daidaito da Firamoinistan.

Shugaban jam’iyyar hamayya ta Democratic Party Lulzim Basha, ya bukaci masu zanga-zanga da su ci gaba har sai Mista Rema ya sauka daga mukaminsa.

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya Æ™irÆ™iri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a Æ™ara wa Æ´an bautar Æ™asa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...